Katin ɗan ƙasa: Kodinetan NIMC a Nasarawa ya buƙaci haɗin kan masu ruwa da tsaki 

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Kodinetan hukumar samar da katin shaidar ɗan ƙasa wato National Identity Management Commission (NIMC) na ƙasa reshen jihar Nasarawa, Zakariah Andekun Ishaku ya buƙaci goyon baya da haɗin kai na musamman tsakanin hukumar da masu ruwa da tsaki ciki har da gwamnatoti a duka matakai don tabbatar an yi wa ɗimbin al’ummar jihar da ma ƙasa bakiɗaya rajistan katunan. 

Kodinetan ya yi kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa dake hanyar Shandam a Lafiya babban birnin jihar a makon da ake ciki.

Zakariah Andekun Ishaya ya nanata muhimmancin samun kati ko lambar shaidar ɗan ƙasan inda ya ƙara da cewa ta haɗin kan ne za a iya cigaba da samun ‘yan Nijeriya da dama waɗanda za su yi rajistar.

Ya cigaba da bayyana cewa “Rajistar NIN na kowa ne kuma wajibi ne ga kowa a ƙasar nan shiyasa muke aiki tukuru don wayar da kawunan al’umma baki ɗaya don kowa ya zo ya yi rajistan bayan sun fahimci mahimmancin hakan kenan don idan basu fahimta ba ba za su ga dalilin yin sa ba. 

“Shi ya sa muke cigaba da wayar da kawunansu don kowanne iyali ya ga amfaninsa da sauran su.

“Kamar yadda ka sani ɗalibai dake son rubuta jarrabawar WAEC da JAMB da sauransu suna buƙatar katin ɗan ƙasa haka suma waɗanda ke neman bayyana a hukumomi daban-daban kamar su bankuna da sauransu ciki har da manoma duk suna buƙatar NIN ɗin don samun tallafin gwamnatin tarayya da sauransu. 

Haka suma nakasassu cikin al’umma suma suna bukatan sa shiyasa gwamnati ta wani shirin ta na musamman da ake kira NASCO tana tara cikakken bayyanen su ta lambobin shedar dan ƙasan nasu don samun saukin tallafa musu a duk lokaci da bukatar hakan ya taso. 

“Har ila yau ina so in yi amfani da damar nan in roƙi gwamnatoti a duka matakai da sarakunan gargajiya da shugabannin addinai su haɗa kai da hukumar NIMC do tabbatar kowa ya yi rajistar katin ɗan ƙasar sa’anan su tabbatar al’ummar nasu suna adana katin da gyau bayan sunyi ragistan don yin amfani dashi a lokuta da suka dace,” inji shi. 

Dangane da wasu nasarori da reshen hukumar a jihar Nasarawa ta cimma a ƙarƙashin jagorancinsa, kodinetan Zakariah Andekun Ishaya ya bayyana cewa duk da bai daɗe da zuwa ba kawo yanzu ya cimma nasarori da suka haɗa da ƙara wayar da kan al’umma game da muhimmancin mallakar katin da ganawa da masu ruwa da tsaki akai-akai da juma haɗa kan ma’aikatansa waje guda inda a yanzu suna aiki tare don cimma burin hukumar kana ya buƙace su su cigaba da hakan.

A ƙarshe duk da kodinetan ya ambato wasu ƙananan ƙalubalai da suke fuskanta a hukumar sai dai ya ce tuni mahukuntan hukumar suka ɗauki ƙwararan matakan shawokan matsalolin da sauransu. 

By ukarofi