Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A ranar Litinin ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta kori ƙarar da aka shigar kan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya, Godwin Emefiele ana neman fansar Naira biliyan 1 kan wahalhalun da tsarin sake fasalin Naira na 2023 ya haifar.
Mai shari’a Inyang Ekwo ne ya yi watsi da ƙarar bisa hujjar cewa wanda ya shigar da ƙarar bai maida hankali kan shari’ar ba.
Wani lauyan mazaunin Abuja, Uthman Tochukwu SAN ne ya shigar da ƙarar, wanda ya zargi waɗanda ake ƙarar da jefa ‘yan Nijeriya cikin wahala mai tsanani ta hanyar wannan shiri na sake fasalin Naira.
ƙarar, mai lamba FHC/ABJ/CS/418/2023, ta haɗa da Buhari da babban lauyan gwamnatin tarayya, da kuma tsohon gwamnan CBN, Emefiele, CBN, da wasu bankunan kasuwanci guda biyu a matsayin waɗanda ake ƙara.
Tochukwu ya yi iƙirarin cewa sake fasalin kuɗin Naira ya jawo masa matsala matuƙa, inda ya yi zargin cewa an tauye masa haƙƙinsa na ’yancin tafiya da kuma mutuncinsa.
Sai dai kuma wanda ya shigar da ƙarar ko lauyansa ba su halarci zaman ba ko kuma bayar da wani uzuri na rashin halartarsu.
Lauyan waɗanda ake ƙara na uku da na huɗu (Emefiele da CBN), Mista Chikelue Amasiani, ya ja hankalin kotun kan yadda mai ƙarar ya ke nuna halin ko-in-kula a kan ƙarar.
Amasiani ya bayar da hujjar cewa tun shigar da karar a 2023, wanda ya shigar da ƙarar da lauyansa ba su nuna wata himma ko kuma da gaske wajen gabatar da ƙarar ba.
Ya buƙaci kotun da ta yi fatali da ƙarar.
A wani ɗan taƙaitaccen hukunci mai shari’a Ekwo ya amince da roƙon lauyan, inda nan take ya kori ƙarar.
