
Daga BELLO A. BABAJI
Jami’an rundunar ƴan sandan farin kaya DSS, sun cafke shahararren ďan ta’adda da ake nema ruwa-a-jallo, Yahaya Zango a sansanin maniyyata a Abuja, yayin da ya yi basaja a matsayin ďaya daga cikinsu don zuwa aikin hajji a ƙasa mai tsarki.
Yahaya Zango ďaya ne daga cikin jaddawalin ƴan ta’adda da hukumomin tsaro suke nema ba dare ba rana bisa hannu a ayyukan fashi da garkuwa da mutane a Arewacin Nijeriya.
An kama shi ne a yayin tantance maniyyatan, a wata motar ‘bus’ ta maniyyata da ta nufi filin jiragen sama, ranar Lahadi.
Wata majiya ta ce, an yi nasarar kama shi ne sakamakon samun waɗansu bayanan sirri, lamarin da ya sa aka bi diddiginsa, inda a nan take ne aka kai shi ofishin hukuma.
Haka kuma wani rahoton ya bayyana cewa, wasu mutane huďu da ake alakanta su da ayyukan ƴan bindiga, suna daga cikin maniyyatan da aka sanya a jaddawalin maniyyatan da za su tafi hajji ta Filin Jiragen Sama na Abuja.
Duk da cewa an kama uku a hanyarsu ta komawa, daga baya an ruwaito cewa an sako ďaya daga ciki.
Saidai, DSS ba ta tabbatar da sahihancin labarin ba a yayin haɗa wannan rahoton.
