
Daga BELLO A. BABAJI
Ministan Ilimi, Tunji Alausa ya sanar da cewa makaratu masu ƙasa da ďalibai 2,000 ba za su sake shiga sahun manyan makarantun da ke cin gajiyar tallafin Hukumar kula da Asusun Tallafa wa Ilimin Manyan Makaratu (TETFUND) ba.
A lokacin da ya ke ganawa da jagororin manyan makarantu a Legas, Ministan ya ce Gwmanatin Tarayya ta ďauki matakin ne domin tabbatar da amfani da dukiyar ƙasa yadda ya dace.
Ya kuma ce, akwai rashin daidaito a yayin da aka bada kuďi daidai ga makaranta mai ďaliban da ba su da yawa da wadda ke da ďalibai mai yawa sosai.
“Makarantun Polytechnics da aka samar a 2019, ďalibai 350 zuwa 550 kaďai suke da su, amma duk da haka suna karbar irin kason da ake bai wa masu ďalibai sama da 18,000”, inji Ministan.
Ya ƙara da cewa, babu shakka TETFUND ta matuƙar amfanar da manyan makarantu ta fuskar ci-gaba a fannoni da dama, don haka ne a karkashin umarnin Shugab Bola Tinubu ake kokarin tabbatar da nagarta kan ayyukan da aka kashe kowane bangare na kuďi a kai.
Har’ilayau, Ministan ya yi tsokaci game da fita karatu da ďalibai ke yi, inda ya ce bincike ya nuna cewa kaso 85 na ire-irensu ba sa dawo wa Nijeriya bayan kammala karatu domin bada gudumawarsu, lamarin da ya sa ya zama wajibi a ķara zuba kuďi wajen inganta harkokin karatu a nan gida Nijeriya.
