Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta ƙalubalanci gwamna Dauda Lawal bisa Kasa cika alƙawarin da yayi lokacin gangamin yaƙin neman zaɓe cewar zai kawo ƙarshen ‘y an ta’adda cikin wata biyu idan ya zama gwamnan Jihar.
Hakan na ƙunshe a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Gusau yau Lahadi Wanda sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar Yusuf Idris ya sanyawa hannu.
A cewar sanarwar gwamna Dauda Lawal bai maida hankali wajen inganta yaƙi da yan ta’addan da suka addabi alummar jihar ba.
Jam’iyyar ta bayyana damuwarta bisa yadda ƴan ta’addan ke kaiwa mazauna jihar munanan hare-hare tare da garkuwa da su a ko yaushe ba tare da nuna damuwa gareshi ba daga gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin gwamna Dauda Lawal tun bayan zaɓen shi shekaru biyu da suka wuce.
Haka zalika jam’iyyar ta ƙalubalanci gwamna Dauda Lawal bisa furucin da yayi cewar gwamnatin sa tana ɗaukar nauyin waɗanda ƴan ta’addan suka harba.
“Ya kamata gwamna Dauda Lawal yayi cikakken bayanin adadin mutanen da aka harba domin binciken da mu kayi ya nuna babu wanda aka ɗauki nauyin maganinshi cikin waɗanda ƴan ta’addan suka harba, hasalima sune ke biyan kuɗaɗen yi masu magani”. A cewar jam’iyyar.
Jam’iyyar ta buƙaci gwamna Dauda Lawal da ya nemi gafarar alummar jihar bisa yadda ya Kasa samar masu da tsaron lafiyar su da dukiyoyin su kamar yadda yayi alƙawarin zai yi cikin watanni biyu a lokacin yaƙin neman zaɓen shi.
Acewar sanarwar, gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin gwamna Dauda Lawal ta gaza matuƙa wajen mai da hankali kan yaƙi da ƴan ta’adda.
“Gwamnatin Dauda Lawal ta Kasa matuƙa wajen kawo ƙarshen ‘ƴan ta’adda domin yanayin nuna ko’ in kula da ta keyi abun damuwa ne”. A cewar jam’iyyar.
