Sakkwato: Sojoji sun halaka na hannun daman Turji, Alhaji Shaudo da wasu kwamandojin ƴan ta’adda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar Sojoji ta tabbatar da mutuwar Alhaji Shaudo Alku, wanda babban mataimaki ne ga jagoran ƴan ta’adda, Bello Turji, a yayin wani hari ta sama da dakarun sojoji suka kai a Jihar Sakkwato.

An samu nasarar hakan ne a karkashin jagorancin atisayen sama na ‘Operation Fagge Yama’ a harin da dakarun suka kai a maboyar ƴan bindiga dake kusa da makarantar firamare ta Tunfa a Karamar Hukumar Isa, ranar Assabar.

Rundunar kamar yadda ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce farmakin ya yi sanadin mutuwar Alhaji Alku, wanda babban ďan ta’adda ne da aka gayyato daga Jamhuriyar Nijar da kashe wasu gomman ƴan ta’adda da kwamandojinsu.

Wani mai sharhi kan lamuran tsaro ya ce, kisan Alku zai haifar wa ayyukan ta’addanci babban gibi duba da yadda ake alaķanta shi da hannu da munanan hare-hare da garkuwa da mutane a shiyyar.

Rundunar ta bayyana cewa, farmakin wani yunķuri ne na takaice ayyukan ƴan bindiga da jagorancinsu a kokarin sojoji na magance ta’addanci.

Ana sa ran samar da ķarin bayanai ga al’umma game da lamarin yayin da sojojin suke cigaba da kulawa da kuma zaman dakon abinda ka iya biyowa baya.

By Babaji