Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai rattaba hannu kan dokar rage farashin magunguna da kayayyakin magunguna.
“Za a rage farashin magunguna da kashi 30 cikin 100 zuwa kashi 80 cikin 100,” inji Trump a wani saƙon da ya wallafa a dandalin sada zumunta.
“Za a daidaita farashin a karon farko cikin shekaru da yawa don adalci irin na Amurka”, inji shi.
Shugaban na Amurka ya ce, zai rattaba hannu kan dokar zartarwa, wanda ya ce zai kasance ɗaya daga cikin mafi tasiri a tarihin Amurka, da ƙarfe 9 na safiyar a ranar Litinin.
Kafofin yaɗa labaran Amurka a lokacin sun ruwaito sanarwar za ta shafi farashin magunguna.
Yawancin magunguna a Amurka suna da tsada musamman idan aka kwatanta da sauran ƙasashe.
Trump ya yi yunƙurin rage farashin magunguna a wa’adinsa na farko a kan karagar mulki.
Shirin a lokacin shi ne samar da magunguna da suka haɗa da insulin da EpiPens a rangwame ga mutanen da ke da ƙarancin kuɗin shiga, da kuma yin amfani da farashi mai rahusa na ƙasa da ƙasa wajen biyan wasu magunguna da aka tanada ƙarƙashin shirin inshorar ‘Medicare’ ga manya.
Ba a taɓa aiwatar da shawarar ba saboda adawar doka da ta siyasa.
