Nijeriya ta sake jaddada aniyar magance ambaliyar ruwa

Spread the love

Daga NAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta jaddada ƙudirinta na daƙile illolin ambaliyar ruwa a faɗin Nijeriya, domin kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasar.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ne ya bayyana hakan a wani taro da ministoci da manyan jami’an ma’aikatu da hukumomin da abin ya shafa kan rigakafin magance illar ambaliyar ruwa a Nijeriya.

Akume, wanda ya samu wakilcin babban sakatariyar ayyuka, Dr Nnamdi Maurice Mberi, ya yaba wa ƙoƙarin da ake yi na magance matsalar ambaliyar ruwa da sauyin yanayi.

Ya ce, gwamnatin tarayya tana aiki tuƙuru tare da dukkan matakan gwamnati don magance munanan illolin da yake yi wa ƙasar nan.

“Wannan gwamnatin ta musamman ce wajen magance matsalolin ambaliyar ruwa da sauran batutuwan da suka shafi sauyin yanayi.

“Shugaban ƙasa ya ƙuduri aniyar aiwatar da ingantattun matakai don daƙile barazanar,” inji shi.

Akume ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin da ke da alhakin ayyukan da suka shafi yanayi, kuma ya buƙaci su yi aiki tare da gwamnatin tarayya.

Ya ce, wannan haɗaka na haɗin guiwa na da nufin samar da mafita mai ɗorewa domin tunkarar ƙalubalen ambaliyar ruwa da ke fuskantar ƙasar.

Hukumomin da suka halarci taron sun gabatar da jawabansu tare da bayyana ƙoƙarinsu na haɗin gwiwa wajen shawo kan bala’o’in yanayi yadda ya kamata.

Ministan Muhalli Balarabe Abbas Lawal wanda Darakta Mai Kula da Zaizayar ƙasa da Ambaliyar Ruwa, Dr. Usman Abdullahi Bokani ya wakilta, ya bayyana cewa ma’aikatar ta samar da na’urorin wayar da kan jama’a masu sarrafa kansu a cikin al’ummomi Ashirin da biyu a faɗin kasar nan da kuma jami’an da ke kula da ambaliyar ruwa domin sanar da hukumar game da ambaliyar ruwa.

Shima da yake mayar da martani ga kalaman SGF, Darakta Janar kuma Babban Jami’in Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta ƙasa (NASRDA) Dr. Matthew Olumide Adepoju ya yi ƙarin haske kan cewa hukumar na da na’urorin da za su sa ido kan madatsar ruwan Lagdo da ke Kamaru wanda ke da alhakin ambaliya a Nijeriya.

A cewar Darakta Janar na Hukumar Kula da Ruwa ta Nijeriya (NIHSA) Dr. Umar Ibrahim Mohammed, hukumar na ci gaba da yin haɗin gwiwa da sauran hukumomi.

By ukarofi