Wani mutum ɗan asalin ƙasar ɓietnam wanda ke ikirarin bai taɓa barci ba tun daga shekarar 1962 ya yaɗu a wani bidiyo da ya bayyana a yanar gizo.
Mutumin mai suna Thai Ngoc yace ya kwashe shekaru 61 ba tare da ya rufe idanuwansa da sunan barci.
Wani fitaccen ma’abocin amfani da YouTube mai suna Drew Binsky ne ya wallafa bidiyon a Instagram bayan tattakin da ya yi don ganawa da mutumin har ƙasar ɓietnam.
A bidiyon, an ga mutumin yana shan sigari kuma idanuwansa biyu buɗe duk da kuwa kwance yake a ƙasa.
Jama’a da dama a Instagram sun ce da tuni mutumin ya mutu idan bai yi barci ba na wannan tsawon lokacin.
Wasu kuwa na ganin cewa, jikin ɗan adam ba zai iya jure wannan tsawon shekarun ba tare da ya yi barci ba.
Mahangar masana; wanne lokaci ɗan Adam zai iya ɗauka babu barci?
Kamar yadda Healthline, wata shafin yanar gizo mai bayanai kan kiwon lafiya ya bayyana, mutum na iya fara surkulle da gane-gane idan ya ɗauki dogon lokaci babu barci.
Ya ce, “mafi dogon lokacin da aka taɓa ɗauka babu barci shi ne sa’o’i 264 ko kwanaki 11 a jere. Duk da babu tabbacin tsawon lokacin da ɗan Adam zai iya kwashewa babu barci, babu daɗewa illar rashin barcin ya ke fara nunawa.”
