
Daga BELLO A. BABAJI
Wani mamakon ruwan sama da aka yi a ranar Talata ya yi sanadin tserewar fursunoni bakwai daga gidan gyaran hali na Ilesa dake Jihar Osun sakamakon ruftawar da wani sashe na gininsa ya yi.
Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Ƙasa, NCoS ta ce lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 2:00 na dare a dalilin iska da tsawa yayin mamakon ruwan.
Kakakin hukumar, Umar Abubakar a wata sanarwa, ya ce tuni hukumomi suka ƙaddamar da aikin farauto waɗanda suka tsere domin dawo da su gidan gyaran halin.
Ya ce, Kwantirola Janar na hukumar, Sylvester Ndidi Nwakuche ya umarci a gaggauta gudanar da bincike game da lamarin.
Ya kuma tabbatar wa al’umma cewa, sun haɗa hannu da wasu hukumomi da jagororin al’umma wajen ganin an cimma nasarar kamo su.
Kazalika, ta yi kira ga al’umma su bada hadin-kai wajen ruwaito mata dukkan wani bayani da zai taimaka wajen kamo fursunonin da suka tsere ta lambobi kamar haka: 07087086005
08075050006
09060004598
