
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Talata ne Majalisar Dattawa ta yi karatu na biyu ga ķudirin da ke neman yin kwaskwarima ga dokokin manyan laifuka (sashen kwatowa da gudanarwa) na 2022 da gabatar da bukatar samar da sabuwar hukuma da za ta ɗauki alhakin kula da ķwato haramtattun kadadori.
Sanata Idiat Oluranti Adelabu (Lagas ta Yamma) ta ɗauki nauyin ķudirin, wanda ke neman a inganta tabbatar da gaskiya da adalci wajen kula da kadadorin da aka ķwato ta yadda za a sauke nauyin hakan daga kan hukumomi 18 da ke kula da ɓangaren a dokar da ake aiki da ita a yanzu.
Ta ce, yin kwaskwarimar abu ne mai muhimmanci duba da yadda ake samun shiga aikin juna da rashin inganci akan hakan daga waɗannan hukumomin.
Sanatar ta ƙara da cewa, dokar da ake aiki da ita ta dora alhakin binciken ire-iren batun da gudanarwarsu akan hukumomin EFCC, ICPC da Kwastom, wanda hakan ya haifar da koma-baya wajen bayyana gaskiya da adalci a ayyukansu.
Haka kuma, ta nemi a samar da tsarin kula da kadadorin da aka ķwace da matattarar rahotonsu na bai-ɗaya, tana mai bada misali da ƙasashen Birtaniya, Amurka Australiya da Afirka ta Kudu da suke yi amfani da irin tsarin, lamarin da ya taimaka wajen cimma nasara.
Tuni aka miƙa ķudirin ga kwamitin majalisar kan harkokin shari’a da ƴan ɗan-adam don yin aiki akansa, wanda ake sa ran kammalawa cikin wata guda.
