Hukumar NYSC ta gudanar da taron yaƙi da cin zarafin mata a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Hukumar NYSC reshen jihar Zamfara ta kira taron wayar da kan ɗalibai da aka zaɓa na wasu makarantu a ƙaramar hukumar Gusau ta Jihar Zamfara dangane da yaƙi da cin zarafin mata.

Gangamin da aka gudanar yau Talata nada nufin ƙara wayar da kan jama’a kan batutuwan da suka shafi cin zarafin mata da kuma rashin daidaiton jinsi.

Shirin mai taken “Kashi na farko na gangamin wayar da kan mata da maza” mai taken “kawar da jahilci”, an ƙaddamar da shi ne a makarantar sakandiren mata ta gwamnati (GGDSS) a shiyyar Tudun Wada da ke garin Gusau.

Da yake jawabi a wajen taron, Darakta-Janar na NYSC Birgediya Janar OO Nafiu, wanda Kodinetan NYSC na jihar Zamfara, Mallam Muhammad Lawan Ahmed ya wakilta ya bayyana cewa, matsalolin da suka shafi jinsi sun shafi maza da mata ta fuskar ‘yancinsu, aikinsu, da nauyin da ya rataya a wuyansu.

A cewarsa, cin zarafin da ya danganci jinsi ya wuce cin zarafi na jiki har ya haɗa da cin zarafi na tunani, ya ƙara da cewa irin wannan abu ya keta haƙƙin waɗanda abin ya shafa.

Shugaban masu yi wa ƙasa hidimar NYSC, ya jaddada muhimmancin tabbatar da cewa babu wani mutum, namiji ko yarinya da za a hana su damar walwala .

Ya kuma ƙara da cewa sanin kowa ne mata sune jinsi mafi rauni a tsakanin alumma, ya kuma buƙaci masu ruwa da tsaki da iyaye da su kula da matsalolin jinsin mata a koda yaushe.

Ya ƙara da cewa, “Hukumar NYSC ta hannun ƙungiyoyinta na Corps Gender Vanguard Community Development Service (CDS) ta kasance a sahun gaba wajen yaƙi da cin zarafin mata a yankunan karkara, Yana mai jaddada cewar dole ne kowa da kowa ya tashi tsaye domin yaƙar wannan barazana, musamman a wuraren da mazauna yankunan karkara ke fama da matsalar da ba a san su ba.

A nasa jawabin, Darakta, Sashen haɗin kai da Misis Victoria Sule ta wakilta, ya bayyana jahilci a matsayin tushen matsalolin da suka shafi jinsi a cikin al’umma.

A nashi jawabin fatan alkhairi, shugaban makarantar, Malam Yusuf Sani Muhammad ya godewa hukumar NYSC da ta zaɓi makarantarsa a matsayin wurin gudanar da shirin, inda ya bayyana ta a matsayin mai ilmantarwa.

Ya ƙara da cewa wayar da kan jama’a zai fara a matakin uwa, da kuma taimaka musu wajen nasiha ga mazajensu da kuma kula da ‘ya’yansu a gida.

By ukarofi