
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar ƴan sandan jihar Gombe, ta tabbatar da kama mutane 25 da ake tuhumar su da hannu a kai farmaki ga CSP Adamu Alhaji Idi, wanda ke aiki a babban ofishin hukumar na yankin Kwadon a Ƙaramar Hukumar Yamaltu-Deba dake jihar.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya bayyana hakan a wata sanarwa, ranar Laraba.
Ya ce, wasu gungun ƴan daba da ake kira da ƴan Kalare ne suka lakaɗa wa jami’in duka a lokacin da ya ke tsaka da gudanar da aikinsa na ɗan sanda a cikin garin Kwadon, ranar Talata.
Ya kuma yi tir da harin tare da cewa tuni aka ɗauki matakin bincike domin tabbatar da hukunta dukkan waɗanda aka samu da hannu a laifin.
DSP Buhari Abdullahi ya ƙara da cewa, a yayin harin ne jami’in ya samu raunuka da dama, lamarin da ya sa aka gaggauta kai shi Asibitin Koyarwa dake Gombe, wanda a yanzu ya ke karɓar magani.
Har’ilayau, kwamishinan ƴan sandan jihar, Bello Yahaya ya ziyarci inda lamarin ya faru don tabbatar da lumana da kwanciyar hankali a yankin, inda ya yi kira ga jama’ada su cigabada kasancewa masu bin doka da oda.
A halin yanzu, waɗanda aka kama suna hannun hukumar yayin da ake cigaba da bincike akansu, inda da zarar an kammala za a miƙa su zuwa kotu domin su fuskanci hukuncin doka.
