Ƙungiyar masu shirya fina-Finai ta ƙasa (MOPPAN) ta sanar da rasuwar shugaban ƙungiyar, Mallam Umar Maikuɗi (Cashman), wanda ya rasu yau Laraba bayan gajeriyar rashin lafiya.
Mallam Maikuɗi fitaccen furodusa ne, darakta, kuma jarumi a masana’antar shirya fina-finai ta Najeriya. Kafin rasuwarsa, ya yi aiki a matsayin malami a sashen nazarin fina-finai a Nuhu Bamalli Polytechnic da ke Zaria.
Marigayin ya riƙe muƙamai daban-daban na shugabanci a ƙungiyar MOPPAN kafin a zaɓe shi a matsayin shugaban ƙungiyar a watan Janairun wannan shekara.
Za a gudanar da sallar jana’izarsa gobe Alhamis da ƙarfe 10:00 na safe a Tudun Jukum, Zaria.
Muna addu’ar Allah ya gafarta masa, ya ji ƙansa, ya ba shi rahama madauwami, kuma ya ba iyalansa, masoyansa, da ɗaukacin al’ummar masana’antar fina-finai ta Najeriya haƙurin jure wannan rashi.
