
Daga BELLO A. BABAJI
A daren ranar Laraba ne Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur dake Arewacin London, ta yi nasara akan Manchester United da ci 1 da nema, wanda hakan ya ba ta damar lashe kofin Europa League na kakar 2024/2025.
Ɗan wasa Brennan Johnson ne wanda ya zura kwallon a minti na 42 bayan kuskure da aka samu daga Luke Shaw na Manchester, lamarin da ya ba ta nasara a Filin wasa dake Birnin Bilbao na ƙasar Sifaniya.
Nasarar ta nuna cewa, Tottenham ta samu gurbi a gasar zakarun Nahiyar Turai, wato UEFA Champions League na kakar 2025/2026.
A ɗaya ɓangaren kuwa, Manchester United ba za ta shiga sahun kungiyoyin da za su buga wasannin matakin Nahiyar ba a shekara mai zuwa.
Wannan shi ne karo na farko da Tottenham ta lashe kofi tun bayan da ta lashe na Carabao a watan Fabarairun 2008, sakamakon doke Chelsea da ci 2 da 1 a wasan ƙarshe da ta yi.
