Mataimakin shugaban ƙasa kashim Shettima ne ya jagoranci ayarin don isar da saƙon jajen shugaba Bola Ahmad Tinubu Kan hatsarin mota da ya rutsa da ‘yan tawagar Jihar Kano a kan hanyar Kaduna zuwa Kano.
‘Yan wasan dai na dawowa ne daga gasar wasannin motsa jiki da aka gudanar a Jihar Ogun.
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma jajanta wa iyalai da al’ummomin da bala’in ambaliyar ruwa ya shafa a ƙaramar hukumar Mokwa ta Jihar Neja, da kuma waɗanda suka rasa rayukansu a bala’in.
