Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Bichi, kuma shugaban kwamitin kasafin majalisa, Hon. Abubakar Kabir Abubakar, ya nuna kaɗuwrsa matuƙa dangane da rasuwar ƴan wasa 22 daga cikin tawagar Jihar Kano da ta halarci gasar wasanni ta ƙasa (National Sports Festival) wanda ta gudana a Jihar Ogun sakamakon hatsarin mota.
Hatsarin wanda ya ritsa da su ne a garin Daka Tsalle dake ƙaramar hukumar Kura a hanyarsu ta dawowa gida bayan kammala gasar.
Hon. Abubakar ya ƙara da cewa “Wannnan babban rashi ne ga Jihar Kano da hukumomin wasanni na gida da kuma na Nijeriya baki ɗaya.
‘Waɗannan ƴan wasan sun rasu ne a daidai lokacin da wannan ƙasar ke buƙatarsu sakamakon irin gudunmawar da su ke badawa don haɓaka harkokin wasanni a Najeriya”.
Sannan ya miƙa sakon ta’aziyya ga ‘yan uwa da abokanan arziki da ma kuma hukumar wasananni ta Jihar kano, yana mai cewa yana addu’a Allah ya baiwa ƴan uwansu haƙurin jure rashin.
