Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano ta sake jaddada haramcin gudanar da shagulgulan hawan sallah a lokacin bikin babbar sallah da ke tafe, tana mai danganta matakin da ya shafi tsaro. Wannan sanarwa ta zo ne sa’o’i kaɗan bayan da fadar masarautar Kano ta aike da takarda ga manyan hakimai, tana gayyatar su domin halartar hawan a ranar Laraba, 4 ga Yuni, 2025.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar tare da haɗin guiwar sauran hukumomin tsaro, an taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar bikin Sallah tare da kira ga jama’a da su kiyaye umarnin tsaro da aka bayar.
Rundunar ta ce bayan binciken sirri da aka gudanar, an tabbatar da ci gaba da barazanar da ta sa aka haramta hawanl tun lokacin ƙaramar Sallah.
Sanarwar ta bayyana cewa wasu ɓatagari da masu goyon bayansu na shirin amfani da bikin domin tayar da tarzoma da haddasa hargitsi kamar yadda aka gani a baya. Saboda haka, an haramta hawa dawakai, tseren motoci, ɗaukar makamai ko kaya masu haɗari a bainar jama’a. Rundunar ta kuma shawarci iyaye da su ja kunnen ‘ya’yansu kada su bari a amfani da su wajen aikata ɓarna.
Sai dai wannan umarni ya saɓawa wasiƙar da masarautar Kano ta fitar, wacce sakataren masarauta Alhaji Abba Yusuf ya sanya wa hannu.
Wasiƙar ta gayyaci dukkan manyan hakimai su hallara a gaban Mai Martaba Sarkin Kano a fadarsa a ranar Alhamis, 5 ga Yuni, domin shawarwari da shiri kan yadda za a gudanar da bikin Sallah.
