
Daga BELLO A. BABAJI
Ministam Tsaro, Badaru Abubakar, ya alaƙanta sake samuwar hare-haren mayaƙan Boko Haram akai-akai da babban shirin ƙungiyar na ganin ta hana zaman lafiya a yankin Sahel, lamarin da ya shafi Nijeriya, Mali, Burkina Faso da Nijar.
Badaru ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da manema labarai a Kaduna, ranar Talata, a lokacin da ya kai ziyarar aiki ta kwana biyu a manyan cibiyoyin sojoji dake jihar ciki har da kwalejin NDA da cibiyar fasaha ta sojojin sama da sauransu.
Ya ce, suna aiki tuƙuru wajen ganin sun daƙile ayyukan ƴan ta’addar, inda a sati biyu da suka gabata ne dakarun sojoji suka fara cin galaba akansu wajen kashe da dama daga cikinsu, lamarin da ya taimaka wajen rage kai hare-hare a sansanin sojoji.
Ya kuma bada tabbacin cewa, Gwamnatin Tarayya tana aiki haiƙan wajen ganin ta dakile dukkan barazana da ake samu a fannin tsaro a Nijeriya.
A yayin tsokaci kan hare-haren ƙauyuka a Jihar Benue, Ministan ya bayyana cewa rikicin ya taƙaitu ne tsakanin manoma da makiyaya, yana mai cewa lamarin na da buƙatar a gano musabbabinsa daga tushe da yin sulhu da jagororin waɗanda abin ya shafa domin kawo ƙarshensa.
Kazalika, Badaru ya yaba wa sojoji bisa ƙoƙarinsu na dawo da zaman lafiya a Karamar hukumar Birnin Gwari da sauran yankunan da ka fama da matsalolin tsaro a Kaduna.
Har’ilayau, ya bayyana gamsuwa da matakin ci-gaba na zamani da rundunar sojojin Nijeriya ta samu, wanda ya taimaka wajen dogaro da kayan aiki na cikin gida ga jami’an.
