Kotu ta tsare wani ɗan Tiktok mai shigar mata da kalaman batsa a gidan gyaran hali

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar ta ce finafinai da ɗab’i ta jihar Kano, ta samu nasarar kama Abubakar Kilina, ɗab Tiktok, mai ɗora bidiyoyinsa cikin shigar mata da hukumar ke zargi da rashin tarbiyya da yin kalamai marasa amfani.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar da Abdullahi Sani Sulaiman, jami’in yada labarai na hukumar tace finafinai da ɗab’i ta Jahar Kano, ya fitar a ranar Laraba.

Daga nan ne hukumar ta gurfanar da shi a gaban kotu, inda mai gabatar da ƙara Barista Garzali Maigari Bichi ya karanto wa wanda ake zargi tuhume-tuhumensa kuma nan take ya amsa dukkan zargin da ake yi masa.

Mai shari’a Halima Wali ta kotun da ke No Mana Land, bayan sauraron shari’ar, ta dage zaman zuwa ranar 17 ga watan Yunin 2025.

Sannan ta ba da umarnin ajiye su a gidan gyaran hali har zuwa ranar da za yanke masa hukumci.

Idan ba a manta ba, watannin baya da suka wuce ne, Hukumar tace finafinai da ɗab’i ta Kano ta aike da irin wannan matasa gaban kotu domin ladaftar da su, inda kotu ta sami matasan da laifi.

Daga na ne kotun ta yanke musu hukuncin daurin shekara daya ko zabin biyan tarar kuɗi na Naira 100,000 tare da gabatar da su waɗanda za su karɓe su domin amincewa da sharadin cewa hakan ba za ta kuma faruwa ba.

Babban manufar wannan aiki da hukumar tace finafinai ke yi na tsawon lokaci shi ne domin kawo gyara da dakile rashin tarbiyar da wasu matasa ke nunawa a kafafen sada zumunta a Jihar Kano wanda yin hakan ya ci karo da tsarin al’ada tare da koyarwar addinin Musulunci.

Shugaban Hukumar, Abba Al-Mustapha, ya jaddada aniyarsa ta kawo karshen ayyukan rashin ɗa’a da ke ƙara yawaita a kafafen sada zumunta na zamani.

By ukarofi