Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mai martaba sarkin Katsina Alhaji Dr Abdulmummuni Kabir Usman ya ce rawanin da ke kansa ba shi da wani amfani idan dai ba zai faɗi gaskiya ba.
Sarkin na magana ne a jawabin sa na hawan barikin babban sallah a lokacin da ya kaiwa gwamna Dikko Raɗɗa gaisuwan barka da sallah a tsohon gidan gwamnatin Katsina.
“Idan ba zan faɗi gaskiya ba, wannan rawanin bashi da wani amfani waje na ,sai in cire masu kayan su,” inji Sarkin.
Ya ƙara da cewa”bana tsoron kowa,zan faɗa maka gaskiya sai dai in sama za ta faɗo ta faɗo,”Mai martaba ya ce.
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su riƙa hakuri da juna ,su so juna tare da gyara zukatansu.
Sarkin ya yi addu’ar Allah dawo da alhazzan jihar da na ƙasa baki ɗaya lafiya da fatan addu’ar da suka yi wa jihar za ta amfani al’ummar jihar.
Gwamnan wanda ya sami wakilcin sakataren gwamnatin jihar Barista Abdullahi Garba Faskari yayi kira ga al’ummar jihar da su zauna lafiya tare da sadaukar da kai.
Malam Dikko Raɗɗa ya kuma sanar da kafa kotun tafi da gidan ka ga musu cin iyaka na burtali a wasu sassan jihar.
Ya kuma yabawa jami’an tsaro wajen ƙoƙarin da suke yi na kawo zaman lafiya a jihar.
Dikko ya taya Sarkin Katsina murna babban sallah.
Ya kuma yaba da alhazzai bana ga yadda suka gudanar da ibada su ba tare da wata matsala ba da fatan Allah mai do su lafiya.
