Kwastom ta ɗage haramcin tashin jirage masu zaman kansu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

An samu sauƙi game da al’amarin jirage guda 60 na masu kansu a Nijeriya, a yayin da Hukumar Kwastom (NCS) ta dakatar da hana su tashi bisa zargin su da rashin biyan kuɗin shigowa na tsawon wata guda.

Da farko NCS ta sanar da haramta wa jiragen aiki a Nijeriya kan rashin biyan kuɗaɗen izinin aiki da su a ƙasar, waɗanda a saboda haka ne aka hana su zirga-zirga daga filayen jiragen sama na Murtala Muhammed dake Lagas da kuma Nnamdi Azikwe a Abuja.

Wasu muryoyi sun bayyana cewa, jiragen da aka soke musu yin aiki, galibinsu daga waje aka yi musu rajista, amma kuma suke aiki a Nijeriya.

Kakakin NCS, Dakta Abdullahi Maiwada ya ce masu jiragen sun amince cewa za su biya kuɗaɗen da ake bin su ga Gwamnatin Tarayya nan da wata ɗaya.

Don haka ne aka dakatar da hanu su aiki duba da cewa sun shirya bin sharuɗɗan da dokar ƙasa ta gindaya musu.

By Babaji