
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMET) ta yi hasashen samun ruwan sama da tsawa a Nijeriya daga ranar Lahadi zuwa Talata.
A saƙon hasashen yanayi da ta fitar a ranar Asabar, hukumar ta ce za a samu tsawa da ruwan sama a wasu yankunan jihohin Taraba da Adamawa dake Arewacin Nijeriya.
Haka kuma, a lokacin rana da dare akwai yiwuwar samuwar tsawa da ruwan sama a jihohin Katsina, Kano, Zamfara, Kaduna, Jigawa, Borno, Gombe da Bauchi.
NiMET ta ce, a yammaci kuma an yi hasashen samun tsawa da ruwan sama a yankunan Abuja, Neja, Nasarawa, Kwara, Kogi, Benue da Filato.
A kudancin Nijeriya kuwa, za a samu hadari da yayyafi a lokutan safiya da yammaci a jihohin Oyo, Ogun, Ondo, Ebonyi, Ekiti, Edo, Abia, Imo, Enugu, Anambra, Legas, Akwa-Ibom, Kuros-Riba, Ribas, Delta da Bayelsa.
Har’ilayau, ta bayyana cewa za a samu tsawa a safiyar ranar Litinin a Sakkwato, Zamfara da Bauchi.
Bugu da ƙari, za a yi ruwa da tsawa a yankunan Sakkwato, Zamfara, Taraba, Adamawa, Katsina, Kano, Jigawa, Borno, Bauchi and Kaduna a yammaci.
