
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bisa ayyana 12 ga watan Yuni a matsayin Ranar Dimukraɗiyya a Nijeriya.
Ya bayyana hakan a matsayin matakin gyara kuskuren da aka tafka a tarihin zaɓen shugaban ƙasar a baya da kuma daraja martabar al’ummar Nijeriya.
A lokacin da ya ke jawabi a taron haɗaka na ƴan majalisar dokokin ƙasa a yayin bikin Ranar Dimukraɗiyya, Tinub ya ce matakin abu da ke nuna karramci ga marigayi MKO Abiola, wanda hakan wani ɓangare ne da ke nuna adalcin mulkin dimokraɗiyya.
Ya kuma ce, Buhari ya yi hakan ne duba da cewa ya amince da nasarar Abiola da abokin takararsa Babagana Kingibe a zaɓen na ranar 12 ga watan Yunin 1993, wanda aka ayyana a matsayin mafi tsafta a tarihin ƙasar.
Shugaba Tinubu ya jaddada ƙoƙarinsa wajen ganin ya cigaba da bada kulawa ga tsarin dimokraɗiyya da cigaba da yi wa al’ummar da suka taimaka wajen dawo da mulkin farar hula aiki tuƙuru.
