Ranar Dimukraɗiyya: Tinubu ya isa wajen zaman haɗaka na Majalisar Dokoki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Tinubu yana zauren Majalisar Dokoki a wani taron haɗaka na ƴan majalisar dokoki na Dattawa da Wakilai a yayin da Nijeriya ke bikin cikar ta shekaru 26 na mulkin dimukraɗiyya.

Da dama daga cikin mambobin majalisar suna wajen taron, inda Tinubu ke gabatar wa ƴan Nijeriya jawabi.

Haka kuma za a gudanar da lakcar Ranar Dimukraɗiyya a yammacin yau, inda manyan ƴan siyasa za su yi jawabi game da al’amuran da suka shafi ƙasa.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai gwamnonin Jihohin Imo da Nasarawa, Hope Uzodimma da Abdullahi Sule da ministan Shari’a da suaran masu alfarma.

By Babaji