Rundunar NSCDC a Katsina ta kama matasa uku ɗauke da tabar wiwi

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Hukumar tsaron farin kaya na Civil Defence ta kama wasu matasa ɗauke da tabar wiwi a unguwar Kofar Bai cikin birnin Katsina.

Kamar yadda jami’in huɗɗa da jama’a na hukumar SC Buhari Hamisu ya ce, jami’an tsaron sun kai farmaki a wani kango bayan samun bayanan sirri na maɓoyan waɗannan miyagun matasa.

A binciken ta, hukumar tsaron farin kayan ta same su ɗauke da tabar wiwi sunƙi 39 da kuma wanda ba a naɗa ba maƙare a ajiye,kamar yadda SC Buhari ya sanar.

Matasan sun haɗa da Aliyu Gambo ɗan shekara 19 da Mustapha Hamza ɗan shekara 18 sai Musa Lawal da dukkan su suka amsa laifin su.

Kwamandan hukumar a Katsina Aminu Datti Ahmad ya yaba da ƙoƙari da nuna ƙwarewa da jami’an sa suka nuna wajen kama waɗannan ɓata gari.

Datti Ahmad yayi kira ga al’ummar jihar da su ba hukumar haɗin kai wajen yaƙi da irin waɗannan miyagun mutane.

Ya kuma sha alwashin cigaba da yaƙi da dillalan haramtattun ƙwayoyi da masu yi wa tattalin arziki zangon ƙasa a jihar.

By ukarofi