Mahara sun farmaki babban birnin Benuwai da kashe mutane da dama

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mutane dama sun rasa rayukansu a yayin da wasu kuma suka samu raunuka a lokacin da ƴan bindiga suka far wa al’umma cikin dare a yankin Mtsewnem dake Ƙauyen Akondutyough a Makurɗi, Babban Birnin Jihar Benuwai, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Wata majiya ta ce, maharan sun shiga garin ne da misalin ƙarfe 3 na dare a lokacin da al’umma suke tsaka da bacci inda suka yi harbe-harbe, lamarin da ya haddasa ɓarnar rayuka da dukiyoyi.

Wani ɗan fafutukar ƴancin ɗan-adam mai suna Ukan Kurugh, ya bayyana harin a matsayin abin tsahin hankali da ya hana kwanciyar hankali acikin al’umma duba da yadda a ƴankwanakin na ake samu hare-haren ƴan bindiga akai-akai a sassan.

Ya ce, mahara a jihar suna cigaba da cin karensu ba babbaka duk da cewa akwai hukumomin tsaro na Gwamnatin Tarayya da na gwamnatin jiha acikin al’ummar jihar, lamarin da ya jefa al’umma cikin zaman ɗar-ɗar.

Ya kuma yi jaje ga iyalan waɗanda aka rasa da waɗanda suka samu raunuka a yayin harin tare da yi musu alƙawarin cigaba da faɗakar da gwamnati da wayar da kan al’umma game da ƴancinsu.

Zuwa lokacin kammala haɗa rahoton, ba a samu kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Edet Udeme a waya ba domin bada ba’asi akan al’amarin.

By Babaji