
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa, za ta daina amfani da tarin takardu a ajiyar rahoton bayanan ma’aikata, inda a madadin haka za a koma amfani da su a na’urar kwamfuta kaɗai, lamarin da zai fara aiki daga ranar 31 ga watan Disambar 2025.
Shugabar Ma’aikatar Ma’aikata ta Ƙasa, Dakta Didi Esther Wilson-Jack ta bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a Abuja, a ɗaya daga cikin gaɓoɓin ayyukan Ranar Ma’aikata na Afirka da Satin Ma’aikata.
Ta ce, matakin wani ɓangare ne na shirin zamanantar da harkokin gwamnati da inganta yadda ofisoshin gwamnati za su riƙa aiki a ƙasar, wanda GwamnatinTarayya ke ƙoƙarin tabbatarwa.
Sannan, ta bayyana hakan a matsayin abinda aka samu a ƙarƙashin dabarun kula da Ma’aikatar Ma’aikata da shirin aiwatarwa, wanda aka faro tun a shekarar 2021, kuam wanda zai ƙare a ƙarshen wannan shekarar.
Daktar ta kuma ce, tuni ofishinta ya dakatar da dogaro da takardu tun gabannin ta kama aiki, inda ta ce ana ɗaukar matakai wajen ganin an sanya sauran ma’aikatu da hukumomin gwamnati akan tsarin.
Haka kuma, ta ambaci Ma’aikatar Lafiya da cewa a kwanan nan ta ƙaddamar da tsarin digital a ayyukanta, wanda hakan ya sa ta zama ma’aikata ta 11 da ta ƙaddamar da tsarin.
Kazalika, ta ce sauran ma’aikatu suna ƙoƙarin ganin sun samar da ci-gaban a ƙarƙashinsu, tana mai cewa gwamnatin tana aiki da masu-ruwa-da-tsaki wajen taimakon ma’aikatun da ƙarin kuɗaɗe da kayan aiki daon tabbatar da aiwatar da shi cikin inganci.
