Gwamna Raɗɗa ya yaba wa jaruman Dimukraɗiyya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya sake tabbatar wa al’ummar Jihar Katsina ƙudirin sa na yin aiki da gaskiya, riƙon amana.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake taya al’ummar Katsina da ‘yan Najeriya murnar bikin ranar Dimukraɗiyya ta 2025.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana 12 ga Yuni a matsayin ranar tuni mai tsarki, cewa kowacce murya ta ɗan ƙasa tana da mahimmanci, kuma kowane fata yana buƙatar goyon bayan gwamnati.

Gwamnan ya yi jinjina a kan sadaukarwar jaruman Dimukraɗiyya, musamman Marigayi Cif MKO Abiola da Bashir Tofa wanda umarnin 12 ga Yuni, 1993 ya zama alamar ikon jama’a na zaɓar shugabanninsu da tsara makomarsu.

“Duk lokacin da na tashi da safe a matsayin Gwamnanku, nakan tuna cewa wannan ofishi ba nawa ba ne – na kowane ɗan ƙasar Katsina ne wanda ya amince da ni da ƙuri’arsa. Ƙoƙarinku nawa ne, fatanku shine ƙarfin hali na,” in ji gwamnan.

Gwamna Raɗɗa ya amince da ƙalubalen da talakawa ke fuskanta a kullum – tun daga matsalolin tattalin arziki zuwa matsalolin tsaro, yana mai basu tabbacin cewa gwamnatinsa tana jin ciwon su kuma tana aiki tuƙuru don samar da sauƙi.

Gwamnan ya jaddada shirye-shiryen gwamnatinsa na mai da hankali kan al’umma, ciki har da shirye-shiryen tallafin noma, ƙarfafa matasa, inganta kiwon lafiya da samar da ababen more rayuwa da suka shafi kowane lungu da saƙo na jihar.

“Dimukradiyya ba ta da ma’ana idan ba ta canza rayuka ba. Shi ya sa muke gina hanyoyi don haɗa al’ummominku, muna tallafa wa manoma don ciyar da iyalai, muna samar da ayyukan yi ga matasanmu, kuma muna tabbatar da ingantaccen kiwon lafiya ya kai ko ina a faɗin jihar,” in ji gwamnan.

Gwamna Raɗɗa ya yi kira ga dukkan ‘yan Najeriya da su kare da kuma inganta Dimukuraɗiyya ta hanyar shiga cikin harkokin mulki da kuma kiyaye haɗin kai duk da bambance-bambance.

Gwamnan ya yi alƙawarin cewa Jihar Katsina za ta ci gaba da zama abin koyi na shugabancin Dimukuraɗiyya, da kuma ci gaba mai haɗaka.

By ukarofi