‘Yan sanda a Katsina sun kama ‘yan ta’adda da suka yi garkuwa da yarinya

Spread the love

‘

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

‘Yan Sanda a Katsina ta tarwatsa sansanin ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa tare da kama mutum huɗu da ceto yarinya ‘yar shekara huɗu.

Jami’in huɗɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana cewa wannan farmaki da suka kai ya biyo bayan ƙorafi da Mustapha Bala da ke zaune a unguwar maɗacin ‘Yan nono a garin Katsina.

DSP Abubakar Sadiq ya ce Mustapha dai ya kai ƙorafin sace ya’yan sa mata ƴan shekara huɗu da kuma 14 ga jami’an ƴan sanda da suka buƙaci ya biya miliyan 50 kafin a saki yaran.

Bayan ƴan sanda sun ɗauki tsawon watanni huɗu suna bincike sa gashi ita yarinyar sa ƴar shekara 14 ta bayyana kanta wajen ƴan sandan inda ta tabbatar masu da cewa ita ce ta ƙirƙira sace kanta da haɗin gwiwar mutane uku suka garkuwa da yarinya yar shekara huɗu,inji DSP Sadiq.

Tuni ƴan sanda suka kama sauran mutane uku waɗanda matasa ne yan shekara 25,19,16 da dukan su suka amsa aikata laifin, yanzu haka suna hannun ƴan sanda ana gudanar da bincike kamar yadda DSP Abubakar Sadiq ya bayyana.

A farmaki da suka kai a maɓoyan yan ta’addan,yan sanda sun gano bindiga ƙirar AK 47 da albarusai masu rai.

Kwamishinoni yan sanda CP Bello Shehu ya jinjina wa yan sandan da suke sashin bincike kan ta’addanci bisa ƙoƙarin da ƙwarewa da suka nuna wajen kama waɗannan ɓata gari.

Ya ƙara nanata kiran da yake ga al’ummar jihar da su rinka taimakawa jami’an tsaro ta bada sahihan bayyana kan maɓoyan irin wannan miyagun mutane.

By ukarofi