CBEX ya nemi ‘yan Nijeriya su saka Dala 200 don dawo da kuɗaɗen da suka rasa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani dandali na hada-hadar zuba hannun jari da ake kira da CBEX, wanda tsarin Ponzi ne, ya koma kasuwanci a faɗin ƙasar makonni bayan ya dakatar da aiki tare da yin awon gaba da dubban ɗaruruwan daloli mallakar wasu ’yan Nijeriya masu saka hannun jari.

Masu saka hannun jari sun ce an buƙaci su koma dandalin don neman jarin da suka yi asara.

“Wani ya tambaye ni na sake tsunduma kuɗi na cikin shirin CBEX a safiyar yau,” inji ɗaya daga cikin masu zuba jarin.

A cewarsu, masu gudanar da tsarin na Ponzi sun kuma buƙaci masu zuba jari da su biya dala 200 don sanya asusun su ya buƙaci yadda za su cire kuɗaɗe masu tsoka.

“Amma ina ganin wata hanya ce ta sake jawo mutane su shiga cikin shirin damfarar, saboda an nemi mu biya dala 200 don ci gaba da kasuwanci da asusunmu kafin mu iya neman cire kuɗi,” wani mai saka hannun jari ya shaida wa Gazette.

“Don haka, dala 200 na waɗanda suka zuba jari sama da dala 1,000 ne. Duk waɗanda ke ƙasa ana neman su biya dala 100.”

A watan Afrilu, ‘yan Nijeriya da dama ne suka yi asarar kuɗaɗen su sakamakon shirin na Ponzi bayan ya daina aik, wanda ya sa masu zuba jari ba za su iya shiga asusunsu ba.

Lamarin ya haifar da firgici a ko ina wanda ya kai ga mutane sun yashe kayan ofishin dandalin na Ibadan.

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta sanar da kame waɗanda ake zargi da hannu a cikin shirin, inda ta ce an gano kuɗaɗen aƙalla ƙasashe uku zuwa huɗu.

A ci gaba da gudanar da bincike, hukumar EFCC ta bayyana cewa ana neman wasu daga cikin ‘yan Nijeriya da ke da alaƙa da shirin tare da kama wasu mutane biyu a makon da ya gabata.

Sai dai hukumar ta ce ba za ta iya mayar da hannun jarin duk waɗanda abin ya shafa ba.

By ukarofi