Hadimin Tinubu ya yi murabus kan zargin APC na maida Nijeriya tsarin jam’iyya ɗaya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Aliyu Audu, mai ba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara na musamman kan harkokin jama’a, ya sanar da ajiye aiki, inda ya nuna damuwarsa kan shirin jam’iyyar APC na mayar da Nijeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya.

Ya tabbatar da haka a wasiƙar da ya rubuta mai ɗauke da kwanan wata 8 ga Yuni, 2025, wacce ya aika wa shugaban ƙasa ta hannun Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila.

Aliyu Audu ya ƙara da cewa wannan ajiye aiki zai fara aiki ne nan take ba tare da ɓata lokaci ba.

A takardar ajiye aikin, Aliyu ya nuna godiya matuƙa ga Shugaba Tinubu bisa damar da ya ba shi na yin hidima a gwamnatinsa.

Ya ce, “Ina matuƙar godiya gare ka, Shugaban ƙasa, bisa damar da ka ba ni na yi wa wannan kasa hidima ƙarƙashin jagorancinka mai hangen nesa. Abin alfahari ne a gare ni in taka rawa wajen yaɗa manufofin wannan gwamnati.”

Audu ya kuma gode wa tsohon mai ba shugaban kƙsa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale, wanda ya ba da sunansa don naɗa shi muƙamin da ya ajiye.

A cikin wata sanarwa da ya fitar daga baya kan dalilin murabus ɗinsa, Aliyu Audu ya ce ya yanke wannan shawara ne saboda tsayawa bisa gaskiya ba don yiwa gwamnati tawaye ba.

Ya ce, “Na ga maganganu da dama dangane da murabus ɗina, amma ina so in fayyace cewa ba tawaye bane, sai dai saboda tsayawa a kan gaskiya.”

“Ko da yake ba ni da ra’ayi daya da jam’iyyar PDP, amma na ƙi amincewa a yi amfani da ni kai tsaye ko da dabara wajen mayar da Nijeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya. Wannan zai kasance cin amanar ni’imar Allah da kuma dokokin dimokraɗiyya.

“Duba da irin albarkar da Allah ya yi wa Nijeriya musamman a wannan lokaci, wajibi ne a gare mu mu kare adalci, daidaito, da ‘yanci.”

An naɗa Aliyu Audu ne a ranar 26 ga Agusta, 2023, a matsayin mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin jama’a, Tinubu ya amince da naɗin nasa a hukumance a ranar 9 ga Oktoba, 2023.

By ukarofi