Raɗaɗin rayuwa: Gwamnoni sun amince da cire shingayen bincike da rage haraji

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnonin jihohin Nijeriya 36 sun amince da cire shingayen na binciken ababen hawa akan hanyoyi da titina da kuma rage yawan haraji a faɗin ƙasar. Sun yanke shawarar ne a taron ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) a Abuja, wanda aka kammala da safiyar jiya Alhamis.

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, wanda ya karanta sanarwar a ƙarshen taron, ya ce gwamnonin sun ƙuduri aniyar wargaza baragurbin tituna da kuma haraji da dama da suka ce ya haddasa tashin farashin abinci a ƙasar.

Sanarwar ta samu sa hannun shugaban ƙungiyar NGF kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaƙ.

“Zauren ya samu bayani ne daga mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), tare da rakiyar ministocin tsaro, noma, kiwonlafiya, da sufuri, kan tashin farashin abinci da kiwo a faɗin ƙasar nan.

“Bayanin ya nuna cewa yawaitar wuraren binciken ababen hawa, haraji ba bisa ƙa’ida ba, da kuma rashin ababen more rayuwa sune muhimman abubuwan da ke haifar da hauhawar farashin kayayyaki da rashin inganci a tsarin samar da abinci.

“NSA ya lura cewa an kafa wani babban kwamiti na ma’aikatu don magance waɗannan matsalolin kuma ya gabatar da shawarwarinsa don amincewa da dandalin.

“Gwamnoni sun amince da gaggawar lamarin tare da bayyana ƙudurin yin haɗin gwiwa da hukumomin tarayya don daidaita haraji, wargaza shingayen binciken ababen hawa, da inganta zirga-zirgar kayayyaki a faɗin jihohi.”

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, NSA Nuhu Ribadu ya ƙi cewa komai kan sakamakon ganawarsa da gwamnonin.

Taron na gaggawa ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da matsalar rashin tsaro a sassa da dama na ƙasar, inda ake ƙara yin kira ga hukumomin tarayya da na jihohi da su ɗauki matakin bai ɗaya.

By ukarofi