Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
’Yan bindiga sun kashe aƙalla manoma 20 da wasu mutum uku da kuma wani ɗan sinitiri a jihar Katsina.
An kashe mutanen ne a wasu hare-hare daban-daban da aka kai ƙaramar hukumar ƙankara, ɗaya daga cikin yankunan da suka fi fama da ƙalubalen tsaro a jihar.
A cewar wani mazaunin yankin da bai amince a bayyana sunansa ba, “Kimanin kwanaki shida da suka gabata ’yan bindiga suka kai hari ƙauyukan Yargoje, Kwakware, ɗanmarke, Gidan Dawa da kuma Burdugau.
“Sun kashe kusan manoma 20, sun sace wasu sannan suka sace shanun da manoman ke amfani da su wajen huda a gonakin nasu,” inji shi.
Kazalika, wata majiyar ta shaida wa wakilinmu cewa a ranar Litinin ’yan bindiga sun kai hari kauyen Marmara, shi ma da yake karamar hukumar ta ƙankara, inda suka fafata da wasu masu aikin sintiri a yankin da ake kira da C’Watch da wasu ’yan sa-kai, inda suka kashe ɗan sintirin ɗaya sannan suka jikkata masu aikin sa-kai biyu a kusa da ƙauyen.
“Sannan sun samu nasarar shiga ƙauyen Marmara, inda suka kashe mutum uku,” inji majiyar.
Wakilinmu ya kuma gano cewa a dai daren Litinin ɗin, maharan sun farmaki wasu ƙauyuka da ke kusa da Kwakware, inda suka sace mutanen da ba a san adadinsu ba.
Wani mazaunin yankin da shi ma bai amince a bayyana sunansa ba ya ce ƙaruwar hare-hare a ƙaramar hukumar a ’yan kwanakin nan ba zai rasa nasaba da yadda wasu ƙananan hukumomin da ke da makwabtaka da ita suka cimma yarjejeniyar zaman lafiya ba.
“Saboda matuƙar za a samu yarjejeniyar zaman lafiya a wasu wuraren ba a ko ina ba, akwai yiwuwar su farmaki wuraren da ba su da yarjejeniyar zaman lafiyar,” inji shi.
