Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Maigirma Alhaji Isa Abba Shugaban masarautar Sarakunan Kasuwannin Kano, wato Sarkin Kasuwar Singa ya yaba wa haɗaɗɗiyar ƙungiyar kasuwar Singa ƙarƙashin shugabancin shugabanin ƙungiyar ‘yan kasuwar Kano Barista Junaidu Zakari shugaban SIMDA wato Singa Market Development Association wacce shugabanta da goyon bayan Sarkin Kasuwar Singa kuma shugaban sarakunan kasuwannin Kano Alhaji Isa Abba da sauran dattawan kasuwar irin su Alhaji Salisu Sambajo da Alhaji Muhammadu Adakawa da kuma gwamnatin Kano bisa wakilcin Alhaji Wada Sagagi kwamishinan kasuwanci da zuba jari na jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki ‘yan kasuwa shugabanni da sauransu kan irin haɗin kai da goyon baya da aka samu a wannan aiki na tsaftace kasuwar Singa wanda aka yi a ranar Lahadin da ta gabata.
Alhaji Isa Abba Sarkin Kasuwar Singa wanda ke tare da wazirinsa Alhaji Uba Waru, Sarkin Kasuwar ta Singa ya bayyana gamsuwa da farin ciki kan yadda shugaban SIMDA Barista Zakari ya tsaya tsayin daka wajen ganin an aiwatar da wannan shara ta tsaftace kasuwa irinta ta farko a tarihi wanda ya yi kira ga shugaban ƙungiyoyin kasuwanni da makamantansu wajen yin irin wannan aiki na alkairi a duk inda suka samu kansu, inda kuma ya buƙaci ɗaukacin ‘yan kasuwar kan su cigaba da tsaftace wuraren kasuwancinsu da muhalinsu a duk inda suka samu kansu ta hanyar tanadar kwandunan zuba shara a shago ko rumfa ko tebur da sauransu.
Shi ma a jawabin sa shugaban SIMDA Alhaji Junaidu Muhammad Zakari yabawa yan kasuwa ya yi kan haɗin kai da suka bayar wajen amsa kirar ƙungiyar na yarda a rufe kasuwar rana guda don yin wannan shara mai matuƙar muhimmanci a wannan kasuwa ta Singa inda ya yabawa gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf wanda hukumar kula da muhalli da kwashe shara ta Kano suka tsaya tsayin daka wajen wannan aiki ya tafi daidai.
Shi ma a jawabinsa sakataren kwamitin dattawa na kasuwar Malam Hamisu Rabiu Jingau ya ce wannan ba ƙaramin al’amari ba ne a ce kasuwar Singa mai sama da mutane miliyan guda amma kowa ya haƙura ya bada haɗin kai a yi wannan aiki wannan abin tarihi ne inda kuma ya ƙara da cewa yasan gwamna na sane da alƙawarin yin tituna da sa fitilu a kasuwar Singa da sauran abubuwan cigaba tunda gwamna mai faɗa da cikawa ne a cewar shugaban kamfanin Hamir Malam Hamisu Rabiu Hamir. Shugaba nin da kwamishinoni da jami’an gwamnatin da shugabannin al’umma ne da dama ne suka halarci wannan kasuwa ta Singa a wannan rana domin gamsuwa da aikin SIMDA.
