Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Zuri’ar Wangarawa wacce ta samo asali daga babban malamin nan Malam Abdulrahman Zaiti, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Dahiru Yusuf Batsari ta yi taro domin sada zumunci a tsakanin Wangarawa Kano da wajenta kamar dai yadda sakataren ƙungiyar Wangarawa Malam Awaisu Balarabe Madabo ya bayyana a lokacin taron.
Ya ƙara da cewa wannan zuri’a ce mai asali wacce tarihin Kano ba zai kammala ba ba tare da an sa zuri’ar Wangarawa ba sakamakon gundunmawar da suke bayarwa ta fuskar addini da kasuwanci da sauransu.
Shi kuwa Madakin Wangarawan Alhaji Zakari Abdullahi Ata ya bayyana cewa wannan zuri’a ta Abdulrahman Zaiti ta shigo Kano ne sama da shekara 700 tun zamanin Sarkin Kano Yaji Ali wanda aka ba shi labarin cewa an ga wasu baƙi suna sansana ƙasa a lokacin da Abdulrahman Zaiti ya ke yin sujadar sallah sai Sarki ya sa aka kira jagoran Wangarawa Abdulrahman Zaiti ya yi masa bayani ya ce Sallah suke ba sansana ƙasa ba kuma ta na ɗaya daga cikin rukunan Musulunci da suka wajaba ga Musulmi kuma daga nan ne Sheikh Abdulrahman Zaiti ya koyarwa al”umma rukunan na Musulunci da sauran iliman addini kamar yadda Madakin Wangarawan Kano Alhaji Zakari Abdullahi Ata ya bayyana a taron.
