Sai an guje wa karɓar kuɗi a yi zaɓe sannan za a zaɓi  shugabanni nagari a ƙasar nan – Ɗanpass

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

ɗan Saran Kano, Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass fitaccen ɗan kasuwa da yake kuma  harkokin siyasa ya yi gargaɗin cewa muddin al’ummar ƙasar nan musamman talakawa ba su daina karɓar na goro don su yi zaɓe ba za su cigaba da zaɓar mutane da za su riƙa jefa su a wahala.

Ya ce yanzu an gurɓata tsarin tafi da dimukwaraɗiyyar ƙasar nan ba za ka fito ka yi tasiri ba sai kana da kuɗi komai cancantar ka saboda an yunwatar da mutane ba sa tunanin yanayin da za su shiga sai a ba su ɗan wani abu a ce ga abinda za su zaɓa.

Alhaji Gambo ɗanpass ya ce irin mutanen da suke da kishi ba su ake zaɓa ba abin takaici sai a baiwa mutane kuɗi su zaɓi duk wani kwashi kwaraf ya zo ya yi ta wahalar da ‘yan ƙasa. Al’ummar ƙasar nan a tsaya a duba mutum nagari wanda ya cancanta a sa shi a gaba a kowane mataki na zaɓe.

Ya kafa misali da cewa yanzu ga jihar Kano nan ta fita zakka saboda al’umma sun fito sun zaɓi Gwamnan da suke so sun ƙi yarda a saye su da kuɗi ko taliya ga shi yana ta gudanar da ayyukan alkhairi na bunƙasa cigaban jama’a..

Ya ce al’ummar ƙasar nan idan za su dage su tsaya su yi zaɓe na cancanta tun daga sama har ƙasa ba tare da an tauye musu ‘yancin yin sahihin zaɓe ba za a samar da gwamnati mai nagarta da za ta yi aiki tuƙuru domin fitar da Nijeriya da halin da aka jefa ta.

Ya ce yanzu duk matsalolin tsaro dake addabar wasu sassa na ƙasar nan talauci ne da aka ƙara mana yake haddasa domin ba a taɓa zaman lafiya da talauci ko yunwa ba.

Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass ya ce idan aka dawo da tsarin ƙasar nan akan doka da oda aka kyautata tsarin kula da cigaban al’umma aka riƙi gaskiya da amana da tausayi a kowane fanni, shine za a samar da gyara mai inganci.

By ukarofi