Umahi ya soke kwangilar biliyan N35 sashi na ɗaya na hanyar Benin-Sapele-Warri 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan ayyuka, Engr. David Umahi ya bayar da umarnin soke kwangilar sake gina sashe na 1 (Benin-Imasabor) na hanyar Benin-Sapele-Warri, wanda aka baiwa kamfanin Leɓant Construction Ltd a ƙarƙashin tsarin bunƙasa ababen more rayuwa da gyara harajin zuba hannun jari, saboda rashin gudanar da aikin.

Umahi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawarsa da shugabannin kamfanin GELD Construction Ltd da SKECC Nigeria Ltd kan jinkirin aiwatar da aikin hanyar Benin zuwa Sapele zuwa Warri da aka gudanar a ofishinsa.

Sauran mahalarta taron sun haɗa da: ƙaramin Ministan Ayyuka Rt. Hon. Bello Goronyo, babban sakataren ma’aikatar, Engr. Olufunso Adebiyi da daraktocin muhimman sassan ma’aikatar.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun mai ba shi shawara na musamman kan yaɗa labarai, Orji Uchenna Orji, a Abuja, ranar Laraba.

Ministan ya nuna rashin jin daɗinsa game da kasawa da/ko watsi da Messrs Leɓant don cimma abin da ake tsammani a cikin ayyukansu na kwangila dangane da sashin hanyar da aka ba su.

Umahi ya ce, “Muna da sassa uku a can, muna da ɓangaren Leɓant, abin takaici Leɓant bai kai yadda ake tsammani ba, har ma sai da muka shiga tsakani muka roƙi Gwamnan Jihar Edo da ya taimaka Allah ya kawo mana ƙarshen wannan hanya.

“Mun raba kashi biyu mafi muni, muka ce Leɓant ya mayar da hankali a ɓangare ɗaya, yayin da Gwamnan Jihar Edo ya shiga tsakani, wanda a tunanina kusan kilomita 23 ne a kan Naira biliyan 35, kuma ɓangaren da Gwamnan Jihar Edo ya sa baki yana ci gaba da tafiya sosai, Leɓant ya bar wurin.

“Mun ba su jerin wasiƙun faɗakarwa, mun kuma ba su sanarwar ƙarshe, idan aka ba ku sanarwar dakatarwa, ku ne cikin kwanaki 14 ku koma wurin ku fara yin abubuwan da ba ku yi ba.

“Wannan lokacin shine don su sake gyara wurin kuma su yi aiki, amma ba su amsa ba.”

Daga nan ne ministan ya umurci babban sakataren da ya dakatar da aikin yadda ya kamata tare da rubuta musu wasiƙa don auna haɗin gwiwa, sannan kuma ya rubuta bankin su don neman a biya su APG.

Ya sha alwashin shigar da ƙorafi ga Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) haɗin gwiwa idan kamfanin ya gaza biyan buƙatar dawo da kuɗaɗen da suka dace a asusun gwamnati.

Umahi, ya bayyana jin daɗinsa da sakamakon tattaunawar da suka yi da SKECC Nigeria Ltd da Geld Construction Ltd kan buƙatar su ƙara ƙaimi kan sassan aikin hanyar da su ke gudanarwa.

Ya yaba wa Gwamnan Jihar Delta Sheriff Oboreɓwori da takwaransa na Jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, bisa yadda suka yi ta ɗauki tsawon wasu kilomita na wannan hanyar.

Umahi ya ce, “Na kira Gwamnan Jihar Delta, kuma na yaba masa bisa kyakkyawan aikin da yake yi, gadar sama uku a lokaci guda, gadar mai kyau, a ƙasar nan, muna buƙatar irin waɗannan ƙawa.

By ukarofi