2027: Haɗakar Atiku da El-Rufa’i na neman INEC ta yi musu rijistar sabuwar jam’iyya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙungiyar ƴan ɓangaren adawa ta Ƙasa a ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa’i, ta yi aiken takardar neman yi wa sabuwar jam’iyya rajista ga Hukumar Zaɓe (INEC).

Sunan jam’iyyar shine ADA, wato ‘All Democratic Alliance’.

An rubuta takardar ne a ranar 19 ga watan Yuni, inda kuma ta je gaban INEC a washe-gari, lamarin da ke nuna haɗakar ta fi gamsuwa da shi akan haɗewa da wata jam’iyya.

Daga cikin waɗanda suka goyi bayan samar da jam’iyyar akwai tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi da Umar Arɗo, wanda shi ne kodinetan Ƙungiyar League of Northern Democrats kuma mataimaki ga tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo.

Lamarin da aka yi da nufin sauya rashin gamsuwar al’umma game da halin da ake ciki a ƙasar da kuma dakatar da Shugaba Bola Tinubu daga zarcewa a zaɓen 2027.

Hakan ya faru ne kwanaki kaɗan da INEC ta gargaɗi ƙungiyoyin siyasa da cewa babu ɗaga-ƙafa ga take dokokin ƙasa ko na zaɓe a yayin tunkarar zaɓen 2027, don haka sai an bi sharuɗɗan doka kafin hukunci akan al’amuran siyasa.

Takardar aiken tana ɗauke ne da sanya hannayen Shugaban haɗakar na wucin-gadi, Cif Akin A. Rickets da Sakataren wucin-gadi, Abdullahi Elayo.

By Babaji