
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban jam’iyyar PDP na riƙon ƙwarya, Ilya Damagum ya ƙi amincewa da ikirarin Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar, Hon. Debo Ologunagba na cewa jam’iyyar ba ta buƙatar sahalewar INEC game da taron kwamitin majalisar zartarwarta karo na 100, wanda aka shirya a ranar 30 ga watan Yuni, 2025.
Ologunagba ya shaida wa manema labarai hakan a ranar Lahadi cewa PDP za ta yi zaman kamar yadda aka tsara ko da amincewar INEC ko babu.
Saidai, Damagum a sanarwar da ya fitar, ya nesanta kansa da matsayar Sakataren, yana mai cewa kalaman ba sa wakiltar jam’iyyar saboda an yi su ne ba tare da shawara ba.
Ya ce, lallai kalaman ba su samu iko ko amincewar kwamitin ayyuka na jam’iyyar ba.
Ya kuma ce, abin ya ba su mamaki ganin yadda aka gaggauta yaɗa wa manema labarai batun ba tare da bin hanyoyin da jam’iyyar ta tsara ba.
Haka kuma, Damagum ya ce wannan ba shi ne karo na farko da Ologunagba ya ke yin irin haka ba, lamarin da ya kira da bijire wa tsarin yanke hukunci na jam’iyyar.
