Za a warware matsalolin sauyin yanayi ne ta ɗaukar matakai a aikace, inji Shettima

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya yi kira ga ƙasashen duniya da su ɗauki matakan da suka dace wajen magance matsalolin sauyin yanayi.

Shettima ya bayyana hakan a matsayin hatsarin da ya zama wajibi a yi ƙoƙarin kauce masa a aikace.

A cewars, hakan ba abu ne da za a yi shi a ɗakin taro ba, saida yana buƙatar kowace ƙasa ta ɗauki matakin magance nata bisa la’akari da matsalolin da ta ke fuskanta a fannin.

Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin ƙaddamar da shirin inganta muhalli na ‘Green Legacy Initiative’ da aka yi a Addis Ababa, Babban Birnin Habasha, inda ya yaba wa ƙasar kan yadda da tunkari matsalolin sauyin yanayi da zimma kuma wanda aka bayyana a fili ga al’umma.

A sanarwar da Kakakinsa, Stanley Nkwocha ya fitar, Shettima, wanda ya je ƙasar ziyarar aiki bayan gayyatar Shugaba Abiy Ahmed Ali, ya yi kira ga ƙasashe da su bunƙasa shirye-shiryensu na sauyin yanayi ta hanyar ninninka ƙoƙarinsu.

Kazalika, ya jaddada goyon bayansa ga shirin bunƙasa kula da muhallin, wanda aka samar da nufin dasa bishiyu guda biliyan 20 a faɗin ƙasar cikin shekaru huɗu.

By Babaji