An sake zaɓar Eze Anaba na Vanguard a matsayin shugaban Ƙungiyar Editoci ta Ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babban Editan jaridar Vanguard, Charles Eze Anaba ya sake zama shugaban Ƙungiyar Editocin Nijeriya (NGE) a wani karon bayan sake zaɓar sa da aka yi a babban taron ƙungiyar da aka gudanar da ɗakin taro na ƙasa dake Enugu.

Anaba ya sake tale kujerar shugabancin ƙungiyar ne bayan sake naɗa shi da aka yi ba tare da abokin karawa ba, lamarin da ake ganin ya faru ne saboda ƙoƙarinsa a jaograncin muƙamin.

Haka kuma an zaɓi Onuoha Ukoh na jaridar The Sun a matsayin Babban Sakatare da ƙuri’u 218 sakamakon doke Wole Sogunle da Qasim Akinreti masu ƙuri’u 45 da 30.

Sauran waɗanda aka zaɓa sun haɗa da Sabastine Abu da ya samu ƙuri’a 175, wanda hakan ya sa ya doke Mohammed Sanusi Jubrin; Mataimakan Shugaba, Kabiru Alabi (Yamm), Hamza Idris (Arewa) da Sheddy Ozoene (Gabas)

Sai ma’aji, Iyobosa Uwugiaren, wadda ta doke Boma, sai Mataimakin Sakatare, Gabriel Fulajimi Akinadewo da kuma Sakataren Labarai, Charles Kanu.

Sai kuma ƴan kwamiti da aka zaɓo daga shiyyoyi; Moses, Ejiro Umukoro, Olabisi Deji-Folutile, Juliet Bumah, Umoru Ibrahim, Paulyn Ugbodaga, Chinedu Max Egere da Ikpong Essien-Udoh.

By Babaji