
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnoni a Arewacin Nijeriya sun bayyana kaɗuwarsu game da rashin hamshaƙin ɗan kasuwa, Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata, wanda ya rasu yana da shekaru 94 a duniya.
Shugaba ƙungiyar gwamnonin kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya a wani saƙon gaisuwar ta’aziyya a madadin takwarorinsa, ya bayyana rasuwar attajirin ɗan Kanon a matsayin rashi ga Nijeriya baki ɗaya.
Ya ce, marigayin ɗaya ne daga cikin masu kuɗi a Nahiyar Afirka da aka fi girmama su a idon al’umma.
Ya kuma ce, mamacin ya taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da tattalin arziƙin Nijeriya gaba duba da tsarin inganta ɗan adam da ci-gabansu da ya samar.
Gwamna Inuwa ya kuma miƙa ta’aziyya a madadin sauran gwamnonin ga iyalan Ɗantata da Gwamnatin Kano da al’ummar jihar da na ƙasa baki ɗaya.
Daga ƙarshe, ya yi masa addu’ar fatan Allah ya yafe masa kurakuransa gami da saka masa alkhairansa da gidan aljanna.
