Ƙungiyar haɗin kan Funtua ta koka kan lalacewar hanyar Funtua zuwa Ɗandume

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 

Ƙungiyar haɗin kan yankin Funtua ta koka kan yadda hanyar Funtua zuwa Dandume ta lalace gaba ɗaya. Hanyar mai tsawon kilomita 45 ta wuce zuwa Birnin Gwari ta miƙa har zuwa Lagos.

Shugaban ƙungiyar, Kwamred Mannir Suleiman ya yi wannan koke ne a saƙonsa na barka da sallah ga al’ummar jihar ta Katsina.

Ya bayyana cewa, al’ummar yankin Dandume manoma ne kuma sun dogara da wannan hanya wajen fitar da amfani gonar su zuwa wasu jihohin ƙasan har da jihar Legas.

“Amma saboda rashin kyawun hanyar manyan motocin da ke ɗaukar amfanin gonan zuwa waje sun bar zuwa saboda rashin kyawun hanyar wanda hakan ya jawo wa manoman mummunan asara”, inji kwamred Suleiman.

Sai ya yi kira ga gwamnatin jihar, Sanata Dandutse da yan majalisar yaƙin da su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen tunkarar gwamnatin tarayya da ta zo ta gyara ko gina sabon hanyar domin dawo da harkokin noma da kasuwanci a yankin.

Kwamred Suleiman ya yabawa wa gwamna Dikko Raɗɗa kan ƙoƙarin da yake wajen magance ta’addancin da sanya matasa a harkokin tafiyar da gwamnatin sa.

Ya ce, ƙungiyar su a shirye take ta haɗa kai da gwamnatin Dikko Radda wajan bada gudunmawar shawarwari na ci gaban jihar musamman yankin Funtua.

Wannan hanya da ake kira ‘Mutuwa Kusa’ ya janyo mutuwar mutane da dama da salwantar ɗimbin dukiya da ƙaruwar ta’addanci Bama a Dandume ba har yankin Funtua baki ɗaya.

By ukarofi