An saka ranar da jirgi zai fara tashi kai tsaye daga Abuja zuwa Landon

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Jirgin saman Nujeriya Air Peace zai fara gudanar da zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye zuwa filin jirgin saman Heathrow na Landan daga Abuja ranar 26 ga Oktoba, 2025.

Wannan gagarumin nasara da aka samu ya biyo bayan ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi na tabbatar da daidaito a yarjejeniyar balaguron jiragen sama na ƙasa da ƙasa.

Wannan ci gaban ya biyo bayan wata takarda mai mai ɗauke da kwanan wata 1 ga watan Agusta, 2024, wanda Ministan Sufurin Jiragen Sama da Raya Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ya rubuta zuwa ga sakataren harkokin sufuri na Birtaniya, Rt. Hon. Louise Haigh MP.

By ukarofi