
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Matatar mai ta Ɗangote ta sake rage farashin litar fetur ga masu dako daga gare ta daga N880 zuwa N840.
Babban jami’in hulɗa da jama’a na rukunin kamfanin Ɗangote, Anthony Chiejina wata sanarwa ya tabbatar da haka a ranar Litinin.
Ya ce, ragin ya fara aiki ne a ranar 30 ga watan Yuni, 2025.
Hakan wani mataki ne na sauƙaƙe wa al’umma da kuma la’akari da sauye-sauyen farashi da ake samu a kasuwannin cinikayyar ɗanyen mai.
