An binne gawar Alhassan Ɗantata a Baƙi’a da ke Madina

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Rahotanni da ke fitowa daga birnin Madina na ƙasar Saudiyya na nuni da cewa an binne marigayi Alhaji Aminu Ɗantata a maƙabartar Baƙi’a da ke birnin Madinatul Munauwara.

Wanda wannan dai ya kai ga cikar burin marigayin da ya bar wasiyar cewa idan ya rasu a kai gawarsa Madina, abin da kuma ya faranta ran masoyan marigayin da ke a sassa daban-daban na duniya.

By ukarofi