
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An kwantar da tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari a ɗaki na musamman (ICU) wani asibiti a Landan saboda fama da matsananciyar rashin lafiya.
Jaridar ‘TheCable’ ta rawaito daga ‘Empowered Newswire’ cewa, wani makusancin tsohon shugaban ya ce Buhari ya kamu da rashin lafiyar ne a Landan a yayin da ya je domin a duba lafiyarsa.
Rahoton ya ce, an kwantar da Buhari a ɗakin ICU, amma daga bisani aka sallame shi makon da ya gabata.
Kodayake ba a bayyana irin cutar da ke damunsa ba, amma rahotanni sun nuna cewa yana samun sauƙi a Landan ɗin.
Sannan, ana sa ran zai dawo Nijeriya da zarar ya warke gaba ɗaya.
