Ɗantata: Majalisar Dattawa ta ɗage zaman duba Kundin Tsarin Mulki a Arewa maso Yamma

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A ranar Talata ne Majalisar Dattawa ta ɗage shirin sake duba Kundin Tsarin Mulkin shiyyar Arewa maso Yamma, saboda karrama marigayi dattijon ƙasa kuma hamshaƙin ɗan kasuwa, Alhaji Aminu Dantata.

ɗantata, wanda kuma fitaccen mai bayar da agaji ne daga jihar Kano, ya rasu a kwanakin baya a ƙasar Saudiyya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ya tattaro cewa an yi jana’izar ɗantata a birnin Madina na ƙasar Saudiyya, daidai da burinsa.

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ne ya sanar da ɗage zaman majalisar a ranar Talata a Abuja.

Ya bayyana ɗantata a matsayin mutum mai mutuƙar girma wanda gudunmawarsa ga ci gaban ƙasa ya dace a san shi.

“Musamman dangane da shiyyar Arewa maso Yamma da kasa baki ɗaya. Saboda rasuwar fitaccen mai bayar da agaji kuma mai ruwa da tsaki, marigayi Alhaji Aminu Dantata, wanda a halin yanzu aka binne shi a Saudiyya, mun yanke shawarar yin shiru na minti ɗaya domin karrama shi,” inji Akpabio.

Ya kuma ƙara da cewa, an cimma matsayar ɗage zaman ne tare da tuntuɓar masu ruwa da tsaki a shiyyar kuma hakan zai ba da damar ɗage zaman taron na yankin Arewa maso Yamma.

“Mun kuma ƙuduri aniyar ɗage taron tsarin mulki na shiyyar Arewa-maso-Yamma zuwa ranar da za a amince da ita a tsakanin masu ruwa da tsaki na yankin Arewa maso Yamma.

Akpabio ya ce, “Wannan shi ne da zarar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya dawo daga Saudiyya.”

Ya ce, duk da ɗage zaman da aka yi a shiyyar Arewa-maso-Yamma, majalisar dattijai na ci gaba da gudanar da taron jin ra’ayin jama’a na shiyyar na tsawon kwanaki biyu kan batun gyara tsarin mulkin 1999.

“An shirya sauraron ƙarar ne a ranakun 4 da 5 ga watan Yuli kuma za a gudanar da shi lokaci guda a wasu shiyyoyin siyasa guda biyar; Legas (Kudu-Yamma) da Enugu (Kudu-Gabas).

“Ikot Ekpene, Akwa Ibom (Kudu-Kudu), Jos (Arewa-Tsakiya) da Maiduguri (Arewa-Gabas),” inji shi.

By ukarofi