
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya tabbatar cewa yana da mota ƙirar ‘Rolls-Royce’ wadda ba wani bane ya ba shi kyauta.
Wike ya faɗi haka ne da nufin mayar da martani ga tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi na cewa Wiken yana da motar alfarma da ya mallaka saboda rashin gaskiyarsa, kamar yadda ya bayyana a wata hira da gidan talabijin na Channels.
A yayin bai wa Ameachin amsa, Wike ya yi ikirarin cewa ya fito ne daga gidan masu kuɗi ba kamar sa ba da ya fito daga gidan talakawa, inda ya ce motarsa ta marsandi (Mercedes-Benz) da ya ke hawa a lokacin da ya ke ɗalibi a makaranta shi ya saya da kuɗinsa.
Ya kuma ce, mahaifinsa ya kasance manaja ne na kamfanoni da dama don haka kuɗi ba matsalar gidansu ba ce, yana mai jaddada cewa da kuɗinsa ya sayi motar.
Kwana ɗaya kafin taƙaddamar ne Ameachi, wanda ya taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, ya bayyana burinsa na sake tsayawa a ƙarƙashin jam’iyyar adawa ta ADC, a hira da Channels.
Ameachi ya bayyana cewa, Tinubu ya gaza kula da harkokin tattalin arziƙin ƙasa inda ya yi ikirarin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta kere ta Tinubu wajen samun nasarori.
